EFCC Arraigns Company Executive for Alleged N72m FraudHausa Translation:EFCC Ta Gurfanar Da Daraktan Kamfani Saboda Zambar N…

EFCC Arraigns Company Executive for Alleged N72m FraudHausa Translation:EFCC Ta Gurfanar Da Daraktan Kamfani Saboda Zambar N…

EFCC Arraigns Company Executive for Alleged N72m Fraud

Hausa Translation:

EFCC Ta Gurfanar Da Daraktan Kamfani Saboda Zambar N72m

Hukumar EFCC reshen Benin ranar Juma’a 6 ga watan Mayu ta gurfanar da Richman Pere da kamfaninshi, Rich Oil Delta West Africa Limited, a gaban mai shari’a Okon Abang na kotun tarayya dake Warri, Jihar Delta akan tuhuma hudu mai alaka da zamba cikin aminci da samar da takardun bogi

EFCC na zarigin Pere manajan kamfanin da zambatar Alhaji Yisa Bello kudi nera miliyan saba’in da biyu inda ya yi karyar cewa zai kawo masa mai.

Ya musanta laifin da ake tuhumar shi da shi.

Mai shari’a Abang ya daga sauraren karar zuwa 29 ga watan Yuni,2022 sannan ya umarci a ajiye shi a gidan gyara halinka.

Ku ziyarci sashen intanet na EFCC a www.efccnigeria.org don karanta karashen labarin.